Iran Tana Fitar Da Kayakin Lantarki Da Injuna Zuwa Kasar Rasha Don Kasuwanci.
Ministan sadarwa da fasahar sadarwa na kasar Iran ya ce Iran fitar da fasahar sadarwa da kayakin da kamfanonin ilmi masu zaman kanasu suke samarwa a kasar zuwa kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Isa Zarepoor ministan fasahar sadawar na kasar Iran yana fadar haka a ziyarar da ya kai kasar ta Rasha a ranar alhamis da ta gabata.
Labarin ya nakalto Isa Zarepour yan afadar haka a shafinsa na yanar gizo a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a karon farko wani kamfanin kirkiro kayakin sadarwa ta zamani ya kulla yarjejeniya da gwamantin kasar Rasha kan yada ilmin da ya gano da kuma shigo da kayakin da yak era zuwa kasar ta Rasha.
READ MORE : General na Sahayoniya; sansanonin sojojin saman Isra’ila za su gurgunta a yakin da ke tafe.
Zarepoor ya kara da cewa kamfanonin kasar Iran ta sadarwa na zamani sun kulla yarjeniya har guda huda da wasu kamfanonin kasar Rasha wanda ya basu damar fadada ayyukansu zuwa kasar Rasha da kuma yankun Eurasia. Da wannan kuma inji ministan kasuwar kasar Iran ta bude a wadannan kasashe.