Iran Tana Da Hakkin Mayar Da Martani Akan Ta’addancin HKI.
Jakadan Iran a MDD ya bayyana cewa; Iran tana da hakkin ta mayar da martani a karkashin doka ta 51 ta hakkin kare ta MDD.”
A ranar Alhamsi ne dai jakadan Iran a MDD Majid Takht-Ravanchi ya rubuta wasika zuwa ga babban magatakardar MDD nbayan wani hari da sojojin HKI su ka kai a kasar Syria wanda ya yi sanadin shahadar masu bayar da shawar ta fuskar soja, Iraniyawa biyu.
Sakon ya kuma kunshi cewa; Masu bayar da shawarar Iraniya suna kasar Syria ne bisa gayyatar gwamnatin wannan kasa, domin taimakawa wajen fada da kuniyar ta’addanci ta ISIS.
Jakadan na Iran a MDD ya cigaba da cewa; Iran tana cikin kasashe nagaba-gaba wadanda su ke fada da ta’addanci wanda hakan yake karkashin dokokin kasa da kasa.
Takht Ravanchi ya bayyana abinda ‘yan sahayoniyar su ka yi a matsayin tsokana kuma laifi da ke cin karo da dokokin kasa da kasa.