Iran Tana Bukata Tabbatar Abubuwa 4 Kafin A Farfado Da JCPOA.
Kakakin gwamnatin kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana bukatan tabbatuwan al-amura masu muhimmanci guda 4 a tattauanwan da ke faraway tsakaninta da kasashen yamma da Amurka dangane da farfado da yarjeniyar JCPOA ta shrin nukliyar kasar.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto Ali Bahador Jahrumi kakakin gwamnatin kasar Iran yana fadar haka a jiya Talata ya kuma kara da cewa, abubuwan sun hada da lamuni, dagawa Iran takunkuman tattalin arziki, da tabbatarwa an dage takunkuman da gaske da kuma rufe maganar binciken wurare da hukumar IAEA tace Iran tana ayyukan makamashin nukliya a cikinsu.
READ MORE : Iran Ta Rubutawa Kasashen Da Suke Daukar Bakwancin Sojojin Amurka A Yankin Wasikar Gargadi.
Jahrami ya kara da cewa, dukkan wadannan al-amura Iran ba zata amince su kasance a takarda kawai ba, dole ne su zama a aikace. Sannan Iran sai ta tabbatar da cewa an dage mata takunkuman da gaske, sannan kamfanonin kasashen waje zasu shiga kasar Iran su ci gaba da ayyukansu ba tare da tsoron cewa za’a dora masu takunkuman tattalin arziki ba. Hakama idan an dage mata takunkuman ba za’a sake dawo da su da watan suna ba.