Kasar jamhuriyar musulunci ta Iran a ta bakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana takaicin ta dangane da yadda kasashen yammacin turai suka taka gagarumar rawa wajen tabbatar da cewa an samu yamutsi a Jamhuriyar musulunci ta Iran din.
Mai magana da yawun ministan harkokin wajen kasar Amir Abdullahian a wata tattaunawa da manema labarai ya bayyana katsalandan gami da kokarin hassala abubuwa da kasashen yammacin turai din sukayi a kwanakin da suka gabata a matsayin babban laifi kuma wanda ya sabawa yarjejeniyar kasa da kasa.
Jami’in diflomasiyyar ya kuma bayyana cewa wannan aikin Allah wadarai da wasu daga kasashen yammacin turan suka aiwatar bazai tafi hakanan ba dole zasu girbi sakamakon ayyukan su ta hanyar karbar hukunci dai dai da abinda suka aikata.
Jami’in ya cigaba da cewa wannan ayyuka na kasashen yammacin turan bai gaza na katsalandan a cikin harkokin cikin gidan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran din ba kuma wannan wani lamari ne wanda Iran din ba zata lamunta ba.
Ana dai zargin kasashen yammacin turai da amurka sunyi uwa sunyi makarbiya a wani yamutsi daya barke a Iran din sakamakon mutuwar wata matashiya, Mahsa Amini wacce ta rasu a hannun jami’an ‘yan sandan Iran din bisa dalilin ciwon zuciya.
Kafafen yada labarai mallakin kasashen turai masu magana da harshen farisanci sun dingi kambama lamarin gami da karin gishiri, lamarin daya tunzura wasu tsirarun mutane a Iran din suka shiga kone kone gami da fashe fashe a tinunan wasu garuruwa amma daga baya al’ummar Iran din sun fito a miliyoyi inda sukayi Allah wadarai da wasu daga cikin ayyukan wadancan mutane wadanda suka hada da kone al’qurani, tutar jamhuriyar musulunci ta Iran gami da kai hari lan dukiyoyin al’umma dana gwamnati.
Rahotanni dain zuwa yanzu na nuni da cewa lamurra sun koma kamar yadda suke a kasar, sai dai jami’ai na nan suna laluben asalin wadanda suka haddasa wannan lamari domin mika su ga mahukunta.