Iran Ta Zargi Isra’ila Da Kawo Cikas A Yunkurin Kawar Da Makaman Kare Dangi A Gabas Ta Tsakiya.
Matamakiyar jakadan kasar Iran a Majalisar dinkin duniya ta yi kira ga majalisar da ta yi matsin lamba kan Isra’ila wajen ganin ta rattaba hannun kan yarjejeniya hana yaduwar makaman kare dangi a NPT.
Da take Magana a gaban kwamitin kula da kwabe dammarar makamai na majalisar dinkin duniya Zahra Ershadi tayi tsokaci game da barazanar da makaman kare dangi suke yi ga rayuwar bil adama. Ya kamata hukumomin kasa da kasa sun hada hannu wuri guda game da abin da ke haifar da rashin zaman lafiya a duniya, ko kuma a fuskanci rikicin siyasa da na soji da suka hada da ci gaba da barazana da yin amafani da makaman kare dangi kan kasashen da basu mallake sub a.
Har ilya yau ta ja hankali game da tsarin da iran ta kikiro a majalisar na ganin an tsaftace yankin daga yaduwar makamai masu linzami, amma Gwamnatin Isra’ila tana kawo cikas wajen ganin an cimma wannan buri, tana tanadin dukkan nauyo’in makaman Karen dangi kuma tana barazanar yin amfani da su kan kaashen yankin
Har yanzu dai Isra’ila ta ki yarda ta bada dama ga masu bincike na hukumar su gudanar da bincike a cibiyoyin ta na soji na nukiliya, balle kuma ta sanya hannun kan yarjejeniyar NPT ta hana yaduwat makaman kare dangi