Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Guterres Kan Take Hakkin Bil’adama A Kasar.
Gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da rahoton babban sakataren MDD António Guterres dangane da take hakkin bil’adama a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Saeed KhadibZadeh yana fadar haka, ya kuma kara da cewa an sanya siyasa a cikin rahoton.
KhadibZadeh ya ce kasar Iran zata ci gaba da aiki da hukumar kare hakkin bil’adama na MDD don akidar gwamnatin kasar ta addinin da kuma bida abinda dokokin kasar suka zayyana kan kare hakkin bil’adama, ba don abinda hukumar kare hakkin bil’adama take gani shi ne kare hakkin bil’adama a wajenta ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa MDD ta tattara bayananta da take hakkin bil’adama ne daga hannin yan ta’adda maikiya JMI, wadanda kuma ba kome ba sai karaya.
Daga karshe KhadibZadeh ya ce, rahoton na MDD ya kasa magana kan takunkuman tattalin arziki na zaluncin da kasashen yamma suka dorawa Iran da kuma tasirinsu kan rayuwar miliyon mutanen kasar Iran. Wadanda suka hada da mutuwar Iraniyawa da dama saboda rashin magunguna da ake samar da su a kasashen yamma kadai.