Iran Ta yi Tir Da Harin Makami Mai Linzamai Da Isra’ila Ta Kai A Kasar Siriya.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi Tir da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa a kasar Siriya ta jaddada cewa wannna mataki day a samu asali daga wuce gona da iri da Tarzoma yana barazanar ga zaman lafiya da tsaron yankin kuma keta dokokin kasa da kasa ne
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saed Khatib Zade ya suka game da gum da baki da kungiyoyin kasa da kasa da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya suka yi kan wadanda suke keta hurumin kasar siriya ta hanyar kai hare-hare
Yace Gum da baki da suke yi zai shafi Darajar kungiyoyin kasa da kasa da Majalisar dinkin duniya wanda ya kamata ace ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta kan wadanda suke keta hurumin kasa siriya dake kawo cikas a kokarin da ta ke yi samar da ci gaba da dawo da tsaro da zaman lafiya a yankin.
Jiragen yakin HKI sun kaddamar da hare-hare da makami mai linzami kan kasar Siriya ta hanyar amfani da sararin samaniyar kasar Labanon ko ta tuddan Golan da ta mamaye
A cikin wani bayani da minsitan harkokin wajen kasar Siriya ta fitar yayi tir da da harin da gwamnatin Isra’ila ta kai kan kasar ,ya ce: “ Siriya za ta ayi amfani da matakai da suka dace wajen mayar da martani kan wuce gona da irin .