Iran Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wata Mujami’a A Najeriya.
Iran ta yi tir da harin da aka kai wata mujami’a, ranar Lahadi a jihar Ondo dake Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gwamman mutane ciki har da mata da yara.
Da yake Allawadai da harin a cikin wata sanarwa, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Saeed Khatibzadeh, ya aike da sakon jaje ga gwamnatin Najeriya da al’ummarta dama iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu.
Mista Khatibzadeh, ya kuma yi kausasan kalamai kan ire iren wadanan ayyukan na rashin imani, wadanda yace ana yin su ne domin haddasa fitina tsakanin addinai.
READ MORE : Barazanar ruwa; Wani mummunan mafarki wanda ya sanya juriya ga Tel Aviv.
Harin na ranar Lahadi data gabata a yayinsa mutane kimanin 50 ne suka rasa rayukansu, da jikkatar wasu da dama yayin da suke ibada a mujami’ar katolika ta St Francis dake garin Owo na jihar Ondo.
READ MORE : ECOWAS Ta Nada Mahamadu Issufu Wakilinta Kan Rikicin Burkina Faso.
READ MORE : Iran Ta Jajantawa Bangaladesh Kan Iftila’in Gobarar Data Kashe Mutum 49.
READ MORE : Yamen; Rayukan Yara 3,182 Suka Salwanta A Cikin Shekaru Takwas.
READ MORE : Kasashen Musulmi Na Tir Da Kalaman Batancin Da Akayi Wa Annabi Muhammad (saw) A Indiya.