Iran Ta yi Maraba Da Yin Aiki Tare Da Hukumar Nukiliya Kan Bunkasa Fasahar Nukiliya.
Mataimakin shugaban kasa na daya ya fadi cewa Iran ba ta neman kira makamin Nukiliya kuma hukuma kula da makamashin nukiliya ta duniya bata iya gabatar da wata hujja dake nuna cewa shirin na iran na ayyukan soji ne.
A lokacin ganawarsa da Darakta janar din hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Mariano Grossi mataimakin shugaban kasa na farko na kasar iran Mohammad Mukhber ya jaddada game da matakin rashin nuna bangare da hukumar ke dauka, yace duniya na tsammanin hukumar ta IAEA ta rika bibiyar shirin nukiliyar kasashen duniya cikin hikima da nuna kwarewa.
Ana sa bangaren Grossi ya fadi cewa yana fatan ziyarar da zai kawo nan gaba a birnin Tehran an fara yin aiki tare kan batun bunkasa fasahar nukiliya ta zaman lafiya a kasar iran .
Daga karshe ya Jaddada cewa dukkan kasashe ciki har da kasar Iran suna da hakkin amfani da fasahar nukiliya a ayyukan lafiya masana’antu da makamashi, yace ayyukan hadin guiwa tsakanin Iran da hukumar zai amfani alummar iran da ma duniya baki daya