Iran ta ce a shirye ta ke ta ci gaba da saidawa gwamnatin Lebanon Mai don taimakata rage karancinsa da take fuskanta, kwanaki bayan isar man fetur din Iran na farko da kungiyar Hizbullah ta tsara shiga kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya ce “Idan gwamnatin Labanon tana son siyan man fetur daga gare su don magance matsalolin da yawan jama’arta ke fuskanta, za su samar mata”
Yayin jawabi ga wani taron manema labarai, jami’in yace tuni Iran ta saidawa wani dan kasuwar Lebanon din man fetur ba tare da ambatar Hizbullah ba.
Hezbollah da ke samun goyon bayan Tehran ta yi alƙawari a watan Agusta cewa zata wadata kasar da man fetur da zata rika daukowa daga Iran, domin rage radadin ƙarancin sa da ke haifar da hargitsi a Labanon, matakin da zai sabawa takunkumin Amurka, kuma alamu sun tabbatar da cewa ba matakin da amurkan zata iya dauka a kan hakan.
Cikin wata tattauna wa da aka samu a fadar shugaban kasar tsakanin Firaminista Mikati da Michel Aoun ya biyo bayan watannin da aka kwashe ana raba mukamai tsakanin bangarorin siyasar kasar.
Mikati ya ce za su yi amfani da duk wata dama da su ke da ita wajen jawo hankalin duk wasu hukumomi na kasashen waje don tabbatar da ganin ana samun cimma bukatu na yau da kullum.
Mikati da aka nada shi mukamin Firaminista a watan Yulin da ya gabata bayan gazawar wasu magabatan sa har su biyu bisa rashin cimma yarjejeniyar wasu batutuwa da aka shirya tuni ya bayyana jerin ministocin da zai yi aiki da su.