Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Ga Duk Wata Barazan A kowanne Mataki.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar iran Majo Janaral Hussaini Salami da yake yawabi a wajen bukin makon kariya na manasa’antu da aka fara a ranar 22 ga watan Agusta da ya samu halartar shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya sha alwashin cewa dakarun tsaron kasar a shirye suke su mayar da martani kan duk wata barazana daga ko ina kuma a kowanne mataki.
A wajen bikin an baje kolin irin nasarorin da kasar ta samu wajen kera makaman kariya da makamai masu linzami da kuma jirage martasa matuki da kasar ta samar a baya bayan nan, kuma ya bayyana ci gaban da iran a samu a bangaren tsaro a matsayi mai girma kuma gagara badau,
Ko a watan jiya ma dakarun sojan sama na kasar Iran sun kai harin gargadi ga wani jirgin mara matuki na Amurka da suka tsinkayoshi yana shawagi a mashigar Hurmuz, Iran a sauko da jirgi mara matuki na Amurka samfurin RQ-4 Global Hawk a watan juni shekara ta 2019 bayan da ya keta hurumin sararin samaniyar kaar iran kuma yayi kunnen uwar shego da gargadin da dakarun sojan sama na iran suka yi masa .