Iran Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimaka Wa Al’ummar Falastinu.
Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian ya bayyana cewa: ba za mu ja da baya daga kare hakkokin al’ummar Iran ba, haka nan kuma ba za mu yi watsi da hakkokin al’ummar musulmin Falastinu ba, za mu ci gaba da ba da goyon baya ga tsayin daka da gwagwarmayar al’ummar Falasdinu don samun ‘yanci.
Wannan dai ya zo ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen kasar ya yi a jiya Litinin tare da wasu gungun malamai, da masana siyasa, da shugabannin bangarorin Falasdinu da na wasu kungiyoyin Labanon, wadanda suka halarci tarukan tunawa da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini a Iran.
Amir Abdollahian ya ce, Imam Khumaini ya kasance yana jaddada cewa Falastinu ita ce batu na farko na duniyar Musulunci.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar goyon bayan gwagwarmayar Falastinawa, kuma duk da matsin lambar da take fuskanta, ba za ta taba ja da baya daga manufofinta ba.
Ya kuma bayyana matakin wasu kasashen musulmi na kulla alaka da sahyoniyawan a matsayin cin amana ga al’ummar Falastinu. Yana mai jaddada cewa wadannan kasashen za su yi nadamar wannan mataki da suka dauka.
Amir Abdollahian ya ci gaba da cewa: Magance matsalar Falasdinu a siyasance ita ce mayar da ‘yan gudun hijirar da kuma gudanar da babban zaben raba gardama wanda ya hada da dukkan ‘yan asalin Falastinu musulmi da kiristoci da kuma yahudawa.