Iran Ta Rubutawa Kasashen Da Suke Daukar Bakwancin Sojojin Amurka A Yankin Wasikar Gargadi.
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya ce ya rubutawa dukkan kasashen yankin tekun farisa wadanda suke daukar bakwancin sojojin kasar Amurka wasika ta gargadi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Muhammad Bakiri yana fadar haka a shafinsa na yanar gizo. Ya kuma kara da cewa an isar da sakon ta ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Bakira ya kara da cewa ya ga yakamata ya gargadi wadannan kasashe ne, saboda yawaitan atisayen sojoji da sintiri a yankin na leken asirin da suka yawaita tsakanin kasashen da kuma sojojin Amurka.
READ MORE : Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Zai Tattauna Da Kasar Qatar Kan Matsalar Makamashi.
Labarin ya kara da cewa Iran ta gargadi gwamnatocin wadannan kasashe kan cewa Iran tana lura da yawan shawajen jiragen yakin Amurka a yakunan tekun farisa da kuma na Omman a cikin yan watannin da suka gabata. Wanda kuma hakan yana nuna cewa ana gudanar da wasu ayyukan leken asiri da kuma bincike cikin lamuran wasu kasashe a yankin. Har’ila yau wannan ya nuna cewa akwai yiyuwan Amurka tare da hadin kai da wadannan kasashen su farwa iran da yaki.
READ MORE : Rashin Tsaro Da Zaman Lafiya A Kasar Yamen Na Shafar Yankin Yammacin Asiya Da Tekun Fasha Kai Tsaye.