Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya ce ya rubutawa dukkan kasashen yankin tekun farisa wadanda suke daukar bakwancin sojojin kasar Amurka wasika ta gargadi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Muhammad Bakiri yana fadar haka a shafinsa na yanar gizo.
Ya kuma kara da cewa an isar da sakon ta ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Bakira ya kara da cewa ya ga yakamata ya gargadi wadannan kasashe ne, saboda yawaitan atisayen sojoji da sintiri a yankin na leken asirin da suka yawaita tsakanin kasashen da kuma sojojin Amurka.
Labarin ya kara da cewa Iran ta gargadi gwamnatocin wadannan kasashe kan cewa Iran tana lura da yawan shawajen jiragen yakin Amurka a yakunan tekun farisa da kuma na Omman a cikin yan watannin da suka gabata. Wanda kuma hakan yana nuna cewa ana gudanar da wasu ayyukan leken asiri da kuma bincike cikin lamuran wasu kasashe a yankin. Har’ila yau wannan ya nuna cewa akwai yiyuwan Amurka tare da hadin kai da wadannan kasashen su farwa iran da yaki.
A wani labarin na daban shugaban na Rasha ya ce sannu a hankali Rasha tana nisantar kuɗaɗen kasashe marasa amana.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau Laraba a gaban babban taron tattalin arzikin Gabashin duniya karo na bakwai, a birnin a birnin Vladivostok na kasar Rasha, shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa, Kudaden ajiya irin su dalar Amurka da Yuro sun rasa amincinsu a matsayin tushen gishikin harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudade ta kasa da kasa.
“Kasashen yammacin duniya sun durkusar da ginshikin tsarin tattalin arzikin duniya, a irin wannan yanayi da kasashen turai suka shiga cikin dambarwa da rashin tabbas a harkokin tattalin arziki, akwai asara idan aka dogara da kudade irin su Dalar Amurka, ko Yurok o kuma Fam na Ingila.
Ya kara da cewa, wannan yanayi ta sa Rasha da sauran kasashe da dama su canza zuwa wasu kudaden na daban, musamman kudin kasar Sin, wato Yuan.
Mataki-mataki muna yin nisa daga yin amfani da waɗannan kuɗaɗen da ba abin doga ba ne hatta ma ga wasu kawayen Amurka, wadanda su ma yanzu sannu a hankali suna rage kudaden ajiyarsu da suka yi da kudin dala.
Putin ya ce yanzu haka, babban kamfanin iskar gas na Rasha wato Gazprom da abokan huldarsa na kasar Sin sun amince su yi mu’amalar kudi a tsakaninsu da ruble na Rasha da kuma yuan na China a cikin kashi 50% na hada-hadar kudadensu.
Source: ABNA HAUSA