Iran, Ta Mika Wa (EU) Matsayarta Game Da Yunkurin Ceto Yarjejeniyar Nukiliya.
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta mika sakonta a rubuce game da shawarwarin karshe da kungiyar tarayyar turai ta gabatar a Vienna na neman ceto yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da kasar a 2015.
Iran, ta ce za’a cimma yarjejeniya idan Amurka da gaske take.
Mohammad Marandi, mashawarci a tawagar tattaunawar ta Iran, ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa, ‘’ran ta bayyana damuwarta, kuma warware ‘yan sabanin da sukayi saura ba abu ne mai wahala ba’’
Ya kara da cewa damuwar da Iran take da shi ne rashin kyakyawar niyya daga bangaren kasashen yamma game da yarjejeniyar, don haka a cewarsa ba zai ce za’a iya cimma yarjejeniya ba, amma mun kusanto cimma matsaya fide da lokutan baya.
READ MORE : Ragowan Sojojin Faransa Na Tawagar Barkhane Sun Fice Daga Mali.
A nan gaba ne ake sa ran ita Amurka za ta mika na ta sakon game da shawarwarin da EU, ta gabatar, kuma a cewar kakakin gwamnatin Amurkar, idan Iran tana shirye wajen mutunta yarjejeniyar gabadayanta, Amurka ma a shirye take.
READ MORE : Lauyoyin Assange Sun Kai Karar CIA Kan Yi Musu Leken Asiri.
READ MORE : Vieira; Akwai Bukatar Kara Zage Dantse Domin Yaki da Wariyar Launin Fata.