Iran Ta Mayar Wa NATO Da Martani Kan Zargin Yin Kutse A Shafukan Yanar Gigo Na Albania.
Iran ta mayar da martani kan bayanin da kungiyar tsaro ta NATO ta fitar, wanda a cikinsa take zargin Iran da yin kutse a cikin wasu shafukan yanar gizo na gwamnatin kasar Albania.
A cikin bayanin da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Burussels na kasar Belgium ya fitar, ya bayyana zargin da cewa ba shi da wani tushe balantana makama.
Bayanin ya kara da cewa, kasar Iran ta fuskanci hare-hare ta hanyar yanar gizo tare da mata barna mai yawa wadda take cutar da al’ummar kasarta, a kan hakan tana adawa da duk wani aiki makamancin wannan domin cutar da wata kasa ko al’ummarta.
Haka nan bayanin ya yi ishara da cewa, wadanda suke aiwatar da irin wadannan ayyuaka na hare-hare ta hanyar yanar gizo a kan kasar Iran kasashe ne wadanda ko dai mambobi ne a cikin kungiyar NATO, ko kuma kawayensu, amma kuma NATO ba ta taba cewa uffan kan hakan ba.
A ranar Laraba da ta gabata ce dai kasar Albania ta sanar da yanke alakar diflomasiyya da kasar Iran, bisa zargin cewa Iran din ta yi kutse a cikin wasu shafukan yanar gizo na kasara cikin watan Yulin da ya gabata.
READ MORE : Gwamnatin Habasha Na Ganawar Sirri Da Mayakan Tigray.
Sai dai a nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta bayyana matakin na gwamnatin Albania da cewa, mataki ne da ba a yi dogon azari da hangen nesa kafin daukarsa ba, domin kuwa ya yi hannun riga da yadda ake tafiyar da alaka ta diflomasiyar kasa da kasa.
READ MORE : Najeriya Na Yunkurin Sasanta Ivory Coast Da Mali.