Iran Ta Mayar Da Martani Game Da Kalaman Biden A Yayin Taron Jeddah.
A yau Lahadi ne ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya yi jiya Asabar daga Saudiyya, yayin taron kasashen Larabawa da Amurka kan tsaro da ci gaba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya ce: Zarge-zargen da shugaban Amurka Joe Biden ya yi a rangadin da yake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, da suka hada da kalaman da ya yi a taron Jeddah, kalaman ba su da tushe balantana makama.
Ya ce wadannan zarge-zarge marasa tushe sun zo ne a ci gaba da kokarin Amurka na haifar da fitina da kuma yada rashin jituwa a tsakanin al’ummomin yankin, yana mai nuni da cewa, Amurka ita ce kadai kasa daya tilo da ta taba yin amfani da makamin nukiliya a kan bil adama, a kan haka ba ta da hurumin yin magana kan shirin Iran na nukiliya na ayyukan farar hula, wanda dukkanin dokokin kasa da kasa suka yarje mata yin hakan.
Baya ga haka kuma ya ce ita ce kasar da take tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen yankin, da kuma yin mamaya da cin zarafi na soji, da sayar da tarin makamai domin haifar da yake-yake.
Kanaani ya ce ya kamata gwamnatocin kasashen yankin su zama cikin fadaka a kowae lokaci, kuma su amsa kiraye-kirayen da Iran take yi musu tsawon lokaci na zuwa ga tattaunawa da hadin gwiwa a yankin da kuma daukar kwararan matakai na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a daukacin gabas ta tsakiya, ba tare da tsoma baki na kasashen duniya ba.