Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bukaci kungiyar Taliban da ta tabbatar da bayar da kariya ga wuraren diflomasiyya da suke cikin birnin Harat da ta kwace iko da shi jiya a kasar Afghanistan.
A cikin wani jawabi da ya fitar a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, hakika Iran ta damu matuka dangane da irin yanayin da kasar Afghanistan ta samu kanta a ciki.
Ya ce birnin Harat wanda shi ne birni na biyu mafi muhimmanci a kasar Afghanistan wanda kuma a halin yanzu ya fada karkashin ikon kungiyar Taliban, ya zama wajibi a kan kungiyar da ta bayar da kariya ga ofisoshin diflomasiyya na kasashen ketare da suke a birnin, da kuma kare rayukan fararen hula, da kuma bayar da kariya ga jami’an diflomasiyya na kasashen waje.
A nata bangaren rundunar sojin kasar Iran ta sanar da cewa, babu wata barazana a kan iyakokin kasar da kuma kasar Afghanistan, komai yana tafiya ba tare da wata matsala ba.
Gwamnatin kasar Iran ta kara jaddada kiranta ga dukkanin bangarori a kasar ta Afghanistan, da hakan ya hada da gwamnatin kasar da kuma kungiyar Taliban, da su rungumi hanyar tattaunawa da kuma warware matsalolin kasar ta hanyar yin sulhu da kuma fahimtar juna.
Kungiyar taliban dai tayi da’awar cewa ta kama garuruwa da dama daga cikin manyan garuruwan kasar ta afganistan.
Ana zargin babban dalilin da ya kawo tashe tashen hankula a kasar ta afganistan baya rasa nasaba da shirin da sojojin amurka sukayi na lalata zaman lafiyar kasar kafin su janye sojojin su.
Kasar jamhuriyar musulunci ta Iran dai na zaman makociyar kasaar afganistan din kuma mai sasanta bangarorin gwamnatin kasar da kuma na kungiyar taliban din.
Jgororin kungiyar taliban din sunyi alkawarin samar da zaman lafiya a kasar ta afganistan amma duk da haka anyi kira gare su da su kula da lafiya gami da rayuwar jami’an diflomasiyya.