Iran Ta Kare Matakin Da Ta Dauka A Kan Kudirin Hukumar IAEA.
Iran ta ce martanin da ta mayar kan kudurin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ta zartar kan shirinta na makamashin nukiliya, ya kasance mai fayyace matsayar da ta dace.
Da yake magana a wani taron manema labarai na mako-mako a yau Litinin a birnin Tehran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya ce kudurin ya haifar da cikas a kan hanyar aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran, wadda a hukumance ake kira da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA).
A ranar Laraba ne majalisar gudanarwa ta hukumar ta IAEA ta amince da wani kuduri da Amurka da kasashen Turai uku da suka kulla yarjejeniyar Iran a shekarar 2015, wato Birtaniya, Faransa, da Jamus suka gabatar, wanda ya zargi Iran da kin hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya.
READ MORE : Kwalara Ta Kashe Sama Da Mutane 150 A Kamaru – MDD.
Abin da ya jawo kudurin shi ne rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar bayan da Darakta Janar nata Rafael Grossi ya kai wata ziyara mai cike da cece-kuce a Isra’ila tare da ganawa da mahukuntan gwamnatin yahudawa a karshen watan jiya.