Iran Ta Kakabawa Amurkawa 24 Takunkumi Bisa Zarginsu Da Keta Dokar Kasar.
Iran ta sanar da sanya takunkumi kan karin jami’ai da daidaikun mutane 24 na kasar Amurka bisa samunsu da laifukan dake shafar ayyukan ta’addanci da keta hakkokin bil Adama.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta fitar ta nuna cewa, mutanen sun taka rawa wajen taimakawa aikata ta’addanci, da kuma keta hakkokin bil Adama.
Hakan ya sanya Iran din, ta sanya mutanen cikin jerin sunayen wadanda ta kakabawa takunkumi, matakin da ya dace da dokokin kare hakkin dan Adam na Iran da dokokin yaki da ayyukan ta’addanci na kasar.
READ MORE : Ramaphosa Da Biden Sun Tattauna Kan Rikicin Rasha Da Ukraine.
Ma’aikatar ta ci gaba da cewa, wadannan mutane sun ba da gudunmawa wajen tallafawa, da shiryawa, da aiwatarwa, da kuma inganta tsauraran matakan da Amurka ta dauka kan al’ummar kasar Iran, da gwamnatin kasar, tare kuma da daukar nauyi da goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da taimakawa miyagun ayyukan da Isra’ila ke kaddamarwa a shiyyar, musamman ma keta hakkokin al’ummar Falastinawa.
READ MORE : Koriya Ta Arewa Ta Caccaki Shugaban Amurka Joe Biden.
READ MORE : Yankin Sahel Zai Samu Tallafin Euro Biliyan 2 Don Kawar Da Yunwa.