Iran Ta Jajantawa Bangaladesh Kan Iftila’in Gobarar Data Kashe Mutum 49.
Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta aike da sakon ta’aziyya da jaje ga kasar Bangaladesh biyo bayan iftila’in gobara da ya auku a kasar.
A sakon da ya aike kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya isa da ta’aziyya ga iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu dama gwamnatin kasar ta Bangaladesh.
Kawo yanzu kimanin mutane 49 ne aka rawaito sun rasa rayukansu a gobarar data biyo bayan fashewar data auku a wata tashar kwantinoni a kusa da birnin Chittagong na kasar Bangladesh
Ko baya ga wadanda suka rasun da akwai sama da 300 da suka jikkata a cewar hukumomin kasar.
Hukumomi sun ce ma’aikatan kashe gobara na cikin wadanda suka mutu.
READ MORE : Yamen; Rayukan Yara 3,182 Suka Salwanta A Cikin Shekaru Takwas.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba amma ana tunanin an ajiye sinadarai ne a cikin wasu daga cikin kwantenonin da ke wurin.
READ MORE : Kasashen Musulmi Na Tir Da Kalaman Batancin Da Akayi Wa Annabi Muhammad (saw) A Indiya.
READ MORE : Nijar; Za A Yi Wa ‘Yan Ta’adda Afuwa Idan Suka Ajiye Makamasu Suka Rungumi Zaman lafiya.
READ MORE : Putin; Rasha Za Ta Ragargaza Makaman Turawa Masu Cin Dogon Zango A Cikin Ukraine.