Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Kokarin Samar Da Hadin Kai tsakanin Kasashen Musulmi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya Saed Khatib Zade ya fadi cewa kasar na aiki tukuru wajen ganin kasashen musulmi sun samu yancin cin gashin kai ta hanyar samar da hadin kai da yin maganar da murya daga da kuma nuna goyon bayan Alummar palestine.
Khatib Zade ya fadi hakan ne a jiya talata jim kadan bayan isarsa kasar Pakistan domin halartar taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta duniya OIC ,
Yace Iran ta yi amanna da hadin kai yin aiki tare da kuma riko da ginshikan al’amuran daya shafi duniyar musulmi akan nuna son kai da kare manufofi na siyasa na kashin kai da kuma bangare daya.
READ MORE : Yaƙi ya jefa mutum 100,000 cikin mawuyacin hali a Mariupol – Ukraine.
Da yake ishara game da batun sake kyautata dagantaka tsakanin Iran da saudiyya kuwa ya bayyana fatansa na ganin alummar yankin sun amfana da kyautatuwar danganta tsakanin kasashen biyu.
A jiya ne aka bude taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi karo na 48 a birnin Islamabad na kasar Pakistan.
READ MORE : Yaƙi ya jefa mutum 100,000 cikin mawuyacin hali a Mariupol – Ukraine.