Iran Ta Ce; Kona Al’kur’ani Mai Girma Da Aka Yi A Kasar sweeden Cin Zarafin Musulmi Biliyan Daya Ne.
Kakakin fadar shugaban kasar Iran Ali Bahadari Jahramy ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Ko kadan hakan baya karkashin hakkin dan’adam.
Jahramy ya kuma ce; Kona al’kur’ani mai girma a cikin watan azumin Ramadan, ba komai ba ne illa nuna kiyayya da gaba ga tsarin raywuar addini ta bil’adama.
Kakakin gwamnatin Iran din ya rubuta a shafinsa na Twitter da safiyar yau Litinin cewa; Yanzu an wayi gari cewa, ‘ yanci yana nufin cin zarafin saukakken addini, kuma hakkin bayyana ra’ayi yana nufin yada tsattsauran ra’ayi da bakin kishi a cikin nahiyar turai.
Tun da fari, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci mai kula da ofishin jakadancin Sweeden a Iran inda ta bayyana masa rashin amincwarta da kona al’kur’ani mai girma da aka yi a kasarsa.
Iran din ta kirayi gwamnatin Sweeden da ta hana irin haka sake afkuwa anan gaba.
READ MORE : Kasashen Musulmi Sun Yi Tir da Hare-haren Da isra’ila Ta Kai Kan Falasdinawa.
A jiya Lahadi ne dai wasu masu tsattsaurin ra’ayi a kasar ta Sweeden su ka kona alkur’ani mai girma.
READ MORE : Matsalar Tsaro; Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP.