Iran Ta Ce Ba Ta Da Wata Alaka Da Maharin Salman Rushdie.
Iran, ta bakin kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar, ta ce ba ta da wata alaka da maharin marubucin nan Salman Rushdi.
Da yake sanar da hakan yayin taron manema labarai na mako mako, Nasser Kanaani, ya ce Iran ba ta da wani labari game da mutumin da ya kai wa Salman Rushdi hari, illah kawai labaren da suka ji daga kafofin yada labaren Amurka.
M. Kanaani, ya kara da cewa kalaman Rushdi, na batanci da na masu goya masa baya su ne suka jamno masa.
« Salman Rushdie, ya janyo wa kansa fishi na al’ummar musulmi da yake bantancin addininsu ta hanyar wuce jan layin da musulmi sama da biliyan daya da rabi ba zasu lamunta da shi ba, kai har ma sauren addinai da suka kadaita ga Allah.
‘’fishin bantancin da ya yi wa musulmi, bata tsaya ga kasar Iran ba kawai, ta harzuka milyoyin musulmai a kasashen duniya daban daban’’ inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.
Wannan dai shi ne martanin farko na Iran a hukumance tun bayan harin wuka da aka kaiwa marubicin Salman Rushdi, wanda aka bayyana cewa ya farfado bayan harin da aka kai masa.