Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Yi Hulda Da Kasashen Africa Wajen Hakar Man Fetur Da Iskar Gas.
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya gana da shugaban Zanzibar, Hussein Mwinyi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama.
Babban jami’in diflomatsiyan na Iran, wanda ke kammala ran gadin nasa a Africa, ya bayyana cewa Iran a shirye take ta yi hulda da kasashen Africa wajen hakar man fetur da iskar gas.
Ya ce duk da takunkuman Amurka kan kasarsa amma Iran ta ci gaba da musaya da kasashen Africa a fannoni daban da daban da suka hada da kiwon lafiya, masana’antu, kimiya da fasaha.
A nasa bangare shugaban kasra ta Zanzibar, Mwinyi, ya jadadda mahimmancin huldar kasuwancin da zuba jari dake tsakanin Iran da kasarsa.
READ MORE : Mayakan Falasdinawa sun kai hari kan motar jami’an tsaron yahudawan sahyoniya.
A karamin ran gadin da ya yi a nahiyar ta Africa, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Amir-Abdollahian, ya ziyarci kasashen Mali da Tanzania, inda ya jadadda mahimanci ci gaban hulda ta tattalin arziki da ci gaba tsakanin kasarsa da kasashen Africa, wanda yana daya daga cikin manyan batutuwan siyasar waje da gwamnatin Iran ta sanya a gaba.
READ MORE : Kotun Saudi Ta Yankewa Tsohon Limamin Ka’aba Daurin Shekara 10 a gidan yari.