Iran Ta Caccaki Sabbin Takunkuman Amurka.
Iran ta yi watsi da takunkuman da Amurka ta kakabawa ma’aikatar leken asirin kasar tana mai cewa ba su da wani tasiri.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya fada a gidan talabijin din kasar cewa “Kamar haramtattun takunkuman da Amurka ta kakaba wa ma’aikatar leken asiri a baya, wannan sabon ma ba zai yi wani tasiri ko kadan ba ga al’amuran jami’an tsaron al’ummar Iran ba.
Jami’in ya kara da cewa, “Bayan goyon bayan Amurka nan take ga zargin karya da gwamnatin Albaniya ta yi wa Iran… ya nuna karara cewa gwamnatin Amurka ce ta tsara wannan lamarin kan Iran.”
A jiya Juma’a ne Amurka ta sanar da kakaba wa ma’aikatar leken asirin kasar Iran da ministanta takunkumi, inda ta zarge su da alaka da wani mummunan harin intanet da aka kai wa Albaniya a watan Yuli.
READ MORE : Aikin karamin ofishin jakadancin Iran a Karbala zai kasance awanni 24 a rana.
Matakin na zuwa ne bayan da Albaniya ta yanke huldar diflomasiyya da Iran a ranar Laraba saboda wannan lamari, inda ta umurci jami’an diflomasiyyar Iran da ma’aikatan ofishin jakadancin su fice cikin sa’o’i 24.
READ MORE : Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3.