Iran Ta Bukaci Kasar Sweden Ta Mutunda Hakin Dan Kasar Wanda Aka Daure Bisa Zalunci.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdullahiyan ya bukaci gwamnatin kasar Sweden ta mutunta hakkin dan kasar Hamid Nouri wanda aka daure shi bisa zalunci a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake ganawa da jakadan kasar Sweden a nan Tehran Mr Mattias Lentz .
Banda haka ministan ya bukaci gwamnatin kasar ta bawa Hamid Nouri damar ganin likitocinsa da kuma karban magani, har’ila da kuma haduwa da iyalansa wadanda zasu zuyarce shi a inda yake tsare.
Jami’an tsaro a kasar Sweden sun kama Hamid Noouri sauka tsare jim kadan bayan isarsa birnin Stockhom a shekara ta 2016
READ MORE : An Bude Taron Tattaunawa Na Kasa A Birnin N’Djamena Na Kasar Chadi.
Iraniyawa yan kungiyar munafukai ta MKO ne suke tuhumarsa da kashe mambebin kungiyar a shekara 1988. Sannan a cikin watan da ya gabata ne wata kotu a kasar ta yanke maa hukuncin daurin rai-da rai tare da shaidar wasu daga cikin munafukan.
READ MORE : Fursunonin Falasdinawa Za su Fara Gudanar da Yajin Cin Abinci Na Gama gari A Gidajen Kurkukun Isra’ila.