Iran Ta Bukaci Hadin Kan Kasashen Musulmi Don Yakar Tsattsauran Ra’ayi.
Ministan harkokin wajen kasar iran Amir abdollahiyan a wata zantawa ta wayar tarho da ya yi da takwaransa na kasar Burunai Dato Erywan yaya jaddada game da bukatar da ake shin a samar da hadin kai tsakanin kasashen musulmi domin yaki da Ta’adanci, kuma sun tattaunawa kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Da ya ke ta ya shi murnar Eidin karamar sallah Amir Abdollahiyan ya bayyana muhimmacin yin aiki tare tsakanin kasahen musulmi na yankin Asiya a bangaren manufofin siyasar waje da sabuwar gwamnatin kasar iran, kana yayi fatan ganawa da ministan wajen na Burnai a birnin Tehran , kuma iran tana marhabin da duk abin da zai kara bukasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Haka zalika bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi game da yanayin da yankin palasdinu yake ciki kana sun yi Tir da laifukan yaki da Isra’ila ke tafakwa kan falasdinawa, Amir Abdollahiyan ya bayyana hadin kan da aka samu tsakanin musulmi a ranar Quds a matsayin babbar alama ta ci gaba da wanzuwar Alummar falasdinu da kuma tsayin daka kan yantar da birnin Quds.
Ana sa bangaren ministan harkokin wajen na Brunei yayi tir da cin zalin Alummar Falasdinu da Isra’ila take yi, tare da nuna goyon bayan gudanar da taron musamman na kungiyar hadin kan kasashen musulmi kan abin da ke faruwa a yankuna da Isra’ila ta mamaye.