Iran; Siriya Ta Tabbatarwa Duniya Kan Cewa Tana Da Ikon Warware Matsalolinta.
Gwamnatin kasar Iran halin da kasar siriya ta fada cikin a cikin shekarun da suka gabata, sanadiyyar shishgin kasashen wajen ne musamman Amurka a cikin harkokin cikin gida na kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana haka a jiya Litinin a taron yan jarida da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin.
Kan’ani ya kara da cewa gwamnatin kasar Siriya ta tabbatarwa duniya kan cewa tana da ikon sake farfadowa daga mummunan halin da kasashen yamma suka jefa kasar a cikin, sannan zata ci gaba da samun nasarori a kan yan ta’adda wadanda kasashen yamma musamman Amurka da kawaynta da yankin suka samar don wargaza kasar.
A shekara ta 2011 ne gwamnatocin Amurka da kawayenta suka samar da kungiyoyin yan ta’adda daban-daban musamman kungiyar Daesh a kasar Siriya da nufin wargazata.
READ MORE : Josep Borrell; Amsar Da Iran Ta Bayar Dangane Da Fardado Da JCPOA Abar Yabawa Ce.
Amma jajircewar sojojin kasar da kuma kawayensu ya wargaza mummunar manufofin wannan kasashen a kasar Siriya.
READ MORE : IRGC; Iran Ta Fara Saida Ingantattun Jiragen Yakin Da Ake Sarrafasu Daga Nesa.
READ MORE : Lebanon; Jami’an Tsaron Isra’ila Suna Shirin Fuskantar Barazar Hizbullah.