Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya yi tafiya a jiya litinin, zuwa lardin Qum mai tsarki, inda ya ziyarci haramin Sayyidah Fatimah Ma’asumah ‘yar Imam Musa Al-Kazim (amincin Allah ya tabbata a gare su) sannan ya hadu da wasu Maraji’in na Addini.
A farkon wannan ziyarar ta yini daya shugaban kasar ya ziyarci ofishin Marja’in addini Ayatullah Husain Nouri Hamedani.
A wannan ganawar, Raisi ya yi nazari kan muhimman matakai da nasarorin da gwamnatin kasar ta cimma duk da makirce-makircen da makiya suka yi na dakatar da samar da kayayyaki da kuma ci gaban da ake samu a kasar. Ya kara da cewa: Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da dukkanin karfinta tare da goyon bayan dukkanin cibiyoyi wajen magance matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, kuma tare da taimakon Ubangiji Madaukakin Sarki a yau Iran ta kara karfi, kuma makiya sun yi rauni fiye da kowane lokaci. ”
A yayin wannan ziyarar shugaban na Iran ya kuma gana da Marja’in addini Ayatullah Jaafar Sobhani, wanda ya yaba da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kuma irin ayyukan da take yi wa al’ummar musulmin Iran. Mai martaba ya bayyana matukar godiyarsa ga shugaban kasar bisa yadda yake nuna sha’awar da yake nunawa kan al’amuran al’adu da suka hada da batun tsafta da Hijabi.
Ayatullahi Sobhani marjain addini, ya yi kira ga gwamnati da ta kara mayar da hankali wajen dakile hauhawar farashin kayayyaki, da daidaita kasuwanni, da hada karfi da karfe, musamman ma kamfanoni masu zaman kansu, a harkokin tattalin arziki.
Bugu da kari, Mr. Raisi ya yi fatan samun bunkasuwa a fannin samar da kayayyaki a cikin gida da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje zai haifar da ingantuwar yanayin tattalin arzikin kasar nan ba da dadewa ba.
Haka nan kuma ya yi ishara da kokarin da makiya suke yi na dakile turbar ci gaba da ci gaban kasa ta hanyar shirya yakin basasa, da sanya tarnaki a fagen samar da kayayyaki, da hana fitar da kayayyakin Iran zuwa kasashen waje, da hana shigo da kudi mai karfi cikin kasar; Ya jaddada cewa “gwamnati ta kuduri aniyar magance wadannan matsaloli tare da shawo kan su, duk da matsin lamba da kalubale.”
Ayatullah Nasser Makarem Shirazi ya kuma tarbi shugaban kasar a ofishinsa da ke lardin Qum a yau; Inda ya yaba da matsayin gwamnatin Iran da shugabanta, “wadanda suka ginu kan yada fata da kuma dogaro ga Ubangiji Madaukakin Sarki wajen fuskantar kalubale da matsaloli.”
Kuma wannan Marja’in addini, Ya kira jami’an kasar kan su yi kokari a samar da ingantattun tsare-tsare na inganta rayuwa da tattalin arziki da rage hauhawar farashin kayayyaki.
Ya kuma jaddada bukatar da ke akwai na dakile kasuwar canji da kuma rage dogaro da kudin dala ta fuskar samar da kwanciyar hankali da inganta yanayin tattalin arzikin da ake ciki tare da kuma warware matsalolin gidaje ta hanyar aiwatar da ayyukan gine-gine da kammala su a cikin ƙayyadaddun lokuta, ta hanyar samar da wadata da kwanciyar hankali ga ‘yan ƙasa.
A daya hannun kuma, shugaban kasar a yayin ziyarar gani da ido da ya kai lardin Qum a jiya litinin, ya halarci bikin karrama ‘yan gwagwarmayar masallatai da ” farfado da littattafan jihadi da gwagwarmaya” da aka gudanar a masallacin Jamkaran. Inda ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana irin rawar da masallatai suke takawa wajen ilmantar da al’umma, da fuskantar gurbacewar tarbiyya, da tunkarar al’amarin tozarta alfarmar Musulunci, musamman Alkur’ani mai girma, wanda aka yi ta maimaitawa a cikin ‘yan kwanakin nan a kasashen yawancin kasashen Turai.
Source: ABNA