Iran; Samar Huldar Jakadanci Tsakanin HKI Da Kasashen Yankin Ba Zai Kawo Zaman Lafiya Ba.
Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa kokarin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isara’ila take yi wajen samar da huldar jakadanci tsakaninda da abinda zata iya na kasashen larabawa ba zai tabbatar da zaman lafiya a yankin ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabin hadin giwa da yake da firai ministan kasar Iraki Mustafa al-kazami wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a jiya Lahadi.
Shugaban ya kara da cewa kasashen Iran da Iran sun yi imani kan cewa kokarin da kasashen yankin Tekun Farisa zasu yi da kansu shi ne zai tabbatar da zaman lafiya a kasashen su da ma yanking aba daya.
READ MORE : Falasdinu; Yara 15 Ne Sojojin Isra’ila Suka Kashe Daga Farkon Wannan Shekarar.
A bangaren dangantaka tsakanin kasashen biyu kuma, Ra’isi ya ce sun tattauna na Al-Kahzimi kan hada garin chalamce ta kudancin kasar Iran da birnin Basra na kasar Iraki da layin dogo. Kuma ana saran hakan zai kara bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
READ MORE : H.K.Isra’ila Ta Fara Mallakawa Yahudawa Yankunan Da Suke Daura Da Masallacin Aksa.