Iran; Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Ci Gaba Da Tattaunawar Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Babban mai shiga tsakani kan batun nukiliyar Iran Ali Bagheri Kani ya tabbatar da cewa “a halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa tare da jami’in Tarayyar Turai, Enrique Moore, domin sanin wuri da lokacin da za a yi shawarwarin na gaba.”
Babban jami’in na Iran Ali Bagheri Kani, ya sanar da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da aiki tare da kodinetan Turai kan shawarwarin nukiliyar, Enrique Mora, domin sanin wuri da lokacin da za a yi shawarwarin na gaba.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar, kuma babban mai shiga tsakani Bagheri Kani ya bayyana a jiya Lahadi cewa, suna gab dad a cimma matsaya a kan wuri da kuma lokacin shawarwarin da ke tafe.
Kamfanin dillancin labaran “Fars” ya nakalto babban mai shiga tsakani na Iran, Bagheri Kani, yana cewa, “tattaunawar Doha an gudanar da ita ne bisa tsari kayyadadde.”
A ‘yan kwanakin da suka gabata Qatar din ta dauki bakuncin tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka da Tarayyar Turai kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a birnin Vienna a shekarar 2015.
Tehran ta tabbatar da cewa tattaunawar Doha tana da kyau, kuma ta bayyana a fili cewa ta “Washington ta bayar da tabbaci kan cewa ba za ta sake janyewa daga yarjejeniyar ba,” yayin da kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana “damuwa da cewa yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015 tana cikin mawuyacin halai, tare da yin kira ga dukaknin bangarori da su yi iyakacin kokarinsu domin kubutar da wannan yarjejeniya.