Masana ilmin kimiyyan sinadarai a nan Iran sun samar da kayakin aiki na gano cutar Covid 19 nau’in Omicron kadai.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa wani kamfanin binciken ilmi magunguna a nan Iran ya sami nasarar samarda kayan gwajin cutar nau’in Omiron tare da amfani da sinadarin sillicon.
Shugaban kamfanin RojeTechnology ya bayyana cewa duk wani nau’i na cutar ta Covid 19 tana da abinda ya bambantata da sauran don haka ya zama wajibi a samar da kayakin aiki na musamman ga kowanne daga cikin nau’in cutar.
Kafin haka ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa Cutar Covid 19 nau’in Omicron yana ci gaba da yaduwa a duniya, kuma ganin yadda yake da hatsari fiye da sauran nau’in cutar, akwai bukatar mutanen su kiyaye dokokin sanya fasila tsakanin mutane, sanan da sanya takunkumin rufe baki, da kuma yin alluran riga kafi zagaye na uku don samun tsaro daga gareta.
Mohammad Bagher Mahmoudi shugaban kamfanin ya kammala da cewa kamfaninsa yana samar da kayakin aikin gwajin cutar, kamar yadda ta samar da na Omicron a halin yanzu.