Iran; Kudaden Shiga A Cikin Watanni 4 Da Suka Gabata Sun Karu Da Kashi 580%
Ministan tattalin arziki kuma kakakin ma’aikatar tattalin arziki na kasar Iran ya bayyana cewa kudaden shiga na gwamnatin kasar daga farkon wannan shekara ta Iraniyawa wato 21 ga watan Maris zuwa yanzu ya karu da kashi 580%.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ehsan Khandouzi yana fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran mai ci ta sami nasarar samun karin kudaden shiga ta hanyar kara yawan danyen man fetur da take sayarwa a cikin watanni 4 da suka gabata.
Khandouzi Ya kara da cewa manufar gwamnatin shugaba Ra’isi a cikin watanni 4 da suka gabata itace rage gibin kasasfin kudi da kuma rage tsadar kayakin a cikin kasuwannin cikin gida.
READ MORE : Mutum Guda Ya Mutu Sa’ilin Zanga Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati A Kasar Sudan.
Dangane da shirin musayar kudaden kasar Iran kai tsaye da kudaden Ruble na kasar Rash aba tare da dalar Amurka ta shiga tsakani ba, ministan ya ce akwai karin labarai masu sa farinciki da muke fatan samu a shekara mai zuwa.
READ MORE : Kasar Turkiya Ta Sake Kai Wani Sabon Hari A Arewacin Kasar Iraqi.