Iran; Kasashe Masu Karfi Na Amfani Da Hakkin Dan Adam Wajen Cimma Muradun Siyasa.
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Saed Khatib Zade da yake ganawa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu a cibiyar kula da tattalin arziki da zamantakewa na majalalisar dinkin duniya ya fadi cewa kare hakkin bil adama yana daya daga cikin abin da ake fakewa dashi wajen cimma manufofin siyasa a dangantakar kasa da kasa
Har il yau ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta bata sunan hakkin dan Adam inda take amfani da shi amatsayin wani makami na cimma manufofinta da hakan ya rusa kimar kare hakki bil adama
Kakakin ya bayyana cewa ma’aikatarsa a shirye take ta taimakawa kungiyoyin domin kare mutunci da matsayinsu ahukumar ECOSOC da ma matakin kasa da kasa.
READ MORE : Mahakan Ma’adanan Burkina Faso Sun Shafe Kusan Wata Guda Makale A Rami.
Sama da kunguyoyin masu zaman kansu guda 80 ne suka halarci wajen taron, inda mataimakin minsitan shari’an na kasar iran kan harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya yi jawabi a wajen taron.
READ MORE : Nijar: Kungiyoyin Farar Hula Sun Koka Kan Batan Dala Miliyan 99 Daga Baitulmali.
READ MORE : Ƙasashen duniya na Allah-wadai da Isra’ila bayan ‘yan sanda sun tarwatsa jana’iza.