Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce makiya suna yaki ne da tattalin arzikin Iran da nufin durkusar da kasar, da kuma rusa hadin kan al’ummar kasa.
“Manufar makiya a wannan yaki ita ce haifar da tabarbarewar tattalin arzikin Iran; nufinsu kenan.
Babu shakka, rugujewar tattalin arziki za ta kasance wani mataki ne na share fage domin sanya al’umma adawa da tsarin Musulunci da kuma aiwatar da munanan manufofinsu na siyasa ta wannan hanya.”
Jagoran dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa kungiyar hadin akn kamfanoni na kasa da kuma ‘yan ‘yan kasuwa na Iran a yau Lahadi.
Ya ce: “A ko da yaushe ina maimaita cewa kada ku sanya sharadi na tattalin arzikin kasa da ayyukan tattalin arziki.
Kada ku dakata kan wani abu da ba mu da shi,” in ji Jagoran, yayin da yake magana kan shawarar da ya ba jami’an gwamnatin kasar game da jajircewa wajen habbaka tattalin arzikin Iran ga sakamakon shawarwarin da aka yi a Vienna.