Jagoran ya tabbatar da Sayyid Ra’isi ɗin a matsayin sabon shugaban ƙasar na Iran ne a wani biki da aka gudanar a yau ɗin nan Talata a Husainiyar Imam Khomeini da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci inda ya sami halartar wasu daga cikin manyan jami’an ƙasar ta Iran.
Shugaban ofishin Jagoran, Hujjatul Islam Sheikh Muhammadi Golpaygani, ne ya karanta ƙudurin Jagoran na tabbatar da Sayyid Ra’isin a matsayin sabon shugaban ƙasar na Iran.
A cikin ƙudurin dai Jagoran ya kirayi sabon shugaban ƙasar da yayi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa irin ƙarfi na cikin gida da ake da shi da kuma share fagen magance matsalolin da ake fuskanta musamman matsalar tattalin arziki.
Har ila yau a cikin ƙudurin kama aikin, Jagoran ya ce: ana buƙatar wani tsari na gudanarwa da zai shigo da irin waɗannan ƙarfi da ƙwarewa na cikin gida da ake da su zuwa ga filin aiki, kawar da dukkanin cikas da suke hana samar da kayayyakin da ake bukata, ƙoƙari wajen aiwatar da siyasar ƙarfafa kuɗin ƙasa da kuma kyautata rayuwar marasa ƙarfi da talakawa da magance musu matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta.
Jagoran ya ci gaba da cewa: A yau ƙasar mu tana buƙatar ayyukan hidima sannan kuma a shirye ta ke a samar da ci gaba a dukkanin fagage. Кasar tana buƙatar tsarin gudanarwa da ta dace, ma’abociyar jihadi da jaruntaka, wacce za ta tsara da kuma aiwatar da ɓoyayyiyar baiwa da damar da ake da ita a ƙasar nan musamman ma ta matasa waɗanda suka ɗara irin matsalolin da ake da su.
Haka nan kuma a jawabin da ya gabatar jim kaɗan bayan miƙa wa sabon shugaban ƙasar takardar kama aikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba da damar ganin wannan rana na miƙa mulki yana mai gode wa al’ummar Iran sakamakon fitowar da suka yi wajen zaɓan sabon shugaban a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.
Jagoran ya ce a ƙasashe da dama miƙa mulki ga sabuwar gwamnati yana tattare da rikici, amma a Iran kan ana gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da nitsuwa ba tare da wani rikici ba.
Don haka Jagoran ya buƙaci sabon shugaban ƙasar da ya gaggauta kafa gwamnatinsa don ta fara aiki tuƙuru wajen magance matsalolin da ake fuskanta.
Imam Khamenei ya buƙaci sabon shugaban ƙasar da ya yi dukkanin abin da zai iya wajen tabbatar da taken kafa ‘gwamnatin jama’a’ da ya dinga rerawa yayin yaƙin neman zaɓe da kuma tabbatar da alaƙa ta ƙut da ƙut tsakanin gwamnatinsa da al’umma.
Yayin da ya ke magana kan matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta kuwa Jagoran ya ce: Magance matsalolin tattalin arziki wani lamari ne da zai ɗau lokaci, kuma tuni al’ummar mu sun san da haka, to sai ya kamata a yi ƙoƙari wajen kajarta lokacin hakan gwargwadon iyawa.
Jagoran ya bayyana fatansa na cewa lalle za a iya magance matsalolin da ake fuskanta sakamakon irin baiwar da Allah Ya yi wa ƙasar ta Iran sai dai ya ce akwai buƙatar a fahimci matsalolin da ake fuskanta ɗin da kuma hanyoyin da za a magance su da kyau, sai kuma a duƙufa wajen aiki tuƙuru.
Daga ƙarshe dai Jagoran yayi addu’a da fatan alheri ga sabuwar gwamnati da kuma shugaban ƙasar wanda ya jinjina wa irin namijin ƙoƙarin da ya yi a baya yayin muƙaman da ya riƙe.
Sabon shugaban na Iran dai ya samu kashi 62% na kuri’un da aka kaɗa wanda ya ba shi damar zama shugaban ƙasar Iran na takwas tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar a shekarar 1979 ƙarƙashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a).
A nasa bangaren sabon shugaban ƙasar Iran Hujjatul Islam Sayyid Ibrahim Ra’isi ya sha alwashin ƙoƙari wajen ɗage takunkumin da Amurka ta sanya wa ƙasar sai dai kuma ya ce ba zai taɓa jingina rayuwar al’ummar ƙasar da kuma tattalin arzikinsu ga buƙatun wasu ‘yan ƙasashen waje ba.
Shugaba Ra’isi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yau ɗin jim kaɗan bayan ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sabon shugaban ƙasar ta Iran daga wajen Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a bikin da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci inda ya sami halartar wasu daga cikin manyan jami’an ƙasar ta Iran.
A jawabin nasa, shugaba Ra’isi ɗan shekaru 60 a duniya kana kuma shugaban ƙasar Iran ɗin na takwas tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar ya bayyana cewar:
“Ko shakka babu za mu yi ƙoƙari wajen ɗage takunkumin zalunci (da aka sanya wa Iran), to sai dai kuma ba za mu taɓa jingina rayuwar al’umma da tattalin arziƙin (mu) ga abin da ‘yan ƙasashen waje suke buƙata ba”, wato yana ishara da Amurka da sauran ƙasashen Turai da suke son ɗamfara wa Iran buƙatunsu cikin tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da manyan ƙasashen duniyan da nufin farfaɗo da yajejeniyar nukilina da aka cimma tsakaninsu da Iran a shekara ta 2015.
Shugaba Ra’isi ya bayyana zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni da ya kai shi ga zama shugaban ƙasar a matsayin wani abu da ke tabbatar da tsarin demokraɗiyya na addini da ke gudana a ƙasar ta Iran inda ya bayyana cewar: Duk da irin baƙar aniya da kuma farfagandar maƙiya ga kuma bala’in annobar nan ta Coronavirus da sauran matsaloli da ake fuskanta amma al’umma sun fito ƙwarai da gaske da kuma baɗa ƙasa a idanuwan maƙya”.
Sabon shugaban na Iran ya ce ya ce irin fitowar da al’umma suka yi yayin zaɓen shugaban ƙasar wani saƙo ne suka isar da neman sauyi da suke da shi, tabbatar da adalci da kuma faɗa da rashawa da cin hanci, talauci da kuma nuna wariya, wanda ya ce zai yi faɗa da hakan da kuma tabbatar da wannan fata da mutane suke da shi.
Don haka Sayyid Ra’isi ya kirayi dukkanin al’ummar ƙasar ta Iran kama daga masana da ƙwararru da sauran jami’ai da dukkanin al’ummar Iran da su haɗa hannu waje guda wajen ganin sun taimaka wa gwamntin tasa wajen cimma manufofin da ta sa a gaba.
Bikin tabbatar da sabon shugaban na Iran ya ƙumshi gabatar da rahoto kan yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar karo na 13 wanda ministan cikin gida na Iran ɗin Abdulridha Rahmani Fadhli ya gabatar da kuma irin matakan da aka ɗauka wajen ganin an gudanar da ingantacce zaɓen.
Tun da fari dai sai ministan cikin gida na Iran din Abdulridha Rahmani Fadhli ya gabatar da rahoto kan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni da irin matakan da aka ɗauka wajen ganin an gudanar da ingantacce zaɓen.
Daga nan kuma sai shugaban ofishin Jagoran, Hujjatul Islam Sheikh Muhammadi Golpaygani, ne ya karanta ƙudurin Jagoran na tabbatar da Sayyid Ra’isin a matsayin sabon shugaban ƙasar na Iran.
A cikin ƙudurin dai Jagoran ya kirayi sabon shugaban ƙasar da yayi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa irin ƙarfi na cikin gida da ake da shi da kuma share fagen magance matsalolin da ake fuskanta musamman matsalar tattalin arziki.