Iran Jagora Ya Bukaci Da A Kara tsananta Matakai Da Za Su Hana Makiya Yin Kutse A Cikin Lamurran Kasa.
Jagoran juyin juya halin musulnci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce makiya suna ci gaba da yakar Iran a bangarori daban-daban, yana mai jaddada bukatar mayar da martani mai cike da sarkakiya a bagarori na siyasa, tsaro, kafafen yada labarai da kuma diflomasiyya.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa, Iran na ci gaba da samun ci gaba mai ban mamaki duk kuwa da makirce-makirce daban-daban da makiya suke kullawa, yana mai hasashen makoma mai haske ga al’ummar Iran.
A kowace shekara a ranar 8 ga Fabrairu, kwamandoji da jami’an sojojin saman Iran suna ganawa da Jagoran domin jaddada mubaya’a mai dimbin tarihi da hafsoshin sojojin saman Iran suka yi tsohon jagoran juyi marigayi Imam Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda suka yi a ranar 8 ga Fabrairun 1979.
Ana kallon taron a matsayin wani sauyi wanda ya bayar da damar kaiwa ga samun nasarar juyin juya halin Musulunci kwanaki uku bayan hakan, wanda ya rufe makomar gwamnatin Pahlawi da Amurka ke marawa baya a Iran.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya yi watsi da da’awar da kasashen yammacin duniya ke yi na bayar da ‘yancin fadin albarkacin baki, tare da bayyana kama-karya a kafafen yada labarai a matsayin daya daga cikin nau’o’in mulkin kama-karya na yammacin Turai.
Ya buga misali da Instagram da sauran shafukan sada zumunta na Amurka wadanda ke yin katsalandan ga suna da hotunan babban kwamandan yaki da ta’addanci na Iran, Janar Qassem Soleimani, wanda aka kashe a harin da jiragen Amurka marasa matuki suka kai a Iraki shekaru biyu da suka wuce.