Iran; IRGC Sun Yi Karin Bayani Kan Yadda Suka Tsare Jiragen Ruwa Na Amurka.
Sojojin ruwa na kasar Iran sun yi karin bayani kan yadda aka yi suka tsare jiragen ruwan Amurka wadanda ake sarrafasu daga nesa don kiyaye karo jiragen a cikin babbar hanyar jiragen ruwa a cikin tekun.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kataparen jirgin ruwan yaki mallakin kasar Iran mai suna ‘Jamaran’ wanda kuma yake aikin sintiri a tekun maliya don hana fashin jirage da kuma duk wata barazanar da zata hana zirga-zirgan jiragen ruwa a cikin taken, ya ga wadannan jiragen ruwa na Amurka sun shiga hanyar da zasu iya hadda hatsarin a cikin tekun.
A nan ne da farko ta kara cibiyoyin Amurka wadanda suke sarrafa jiragen ruwan su yi hankali kada su haddasa hatsari a cikin tekun, amma ba su ga maida martani daga cibiyoyin ba, a nan ne suka kwace iko da sarrafa jirgen suka kuma kama su. Sai dai bayan da suka isa inda babu hatsari suke saki jiragen ruwan marasa matuki, ko wadanda ake sarrafasu daga nesa mallaka gwamnatin Amurka.
Labarin ya kara da cewa wannan ya auku ne kwanaki biyu kacal inda sojojin ruwa na kasar Iran suka kwace wani jirgin ruwa marasa matukin wanda sojojin Amurka suka kuale shi a cikin tekun farisa.
Source