Iran; Idan Aka Amince Da BukatunTa Za’a Shiga Sabon Shafi A Tattaunawar Vieanna.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abadollahiyan a lokacin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Oman Badar Albusaidi ya fadi cewa idan aka mutunta hakkokin Iran da bangaren tattalin arziki a Amsar da Amurka za ta bayar kan bukatun iran to za’a bude sabon shafi a tattaunawar da ake yi a viyanna na cire mata takunkumi
Har ila yau a tattaunawar ta su ta wayar tarho ministocin wajen kasashen iran da Oman sun yi musayar ra’ayi game da tattaunawar da ake yi da akasashe ma’abota karfi na duniya na ganin an cire mata takunkumi kuma sun tattauna kan yadda zasu kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu da kuma abubuwa da manufa ta zo daya a yankin da ma kasa da kasa.
Amir Abdallahian ya jinjinawa kokarin da Oman ta yi wajen nuna goyon bayan irin mataken da ake dauka a tattaunawar da ake yi tsakaninta da kasahen turai na cirewa iran takunkumi da farfado da yarjejniyar nukiliya da aka rattaba hannu a kai
Ana sa bangaren minsitan harkokin wajen Oman Badr Albusairi ya nuna fatansa na gani an fitar da sakamako da zai gamsar da dukkan bangarorin dake tattauwa kan shirin na nukiliya iran ta hanyar hadin guiwa tsakaninsu.