Iran; Hulda Da Afirca Na Daya Daga Cikin Manufofin Siyasarmu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kanaani ya bayyana cewa tafiya zuwa nahiyar Afirca da ministan harkokin wajen kasar ya yi na daya daga cikin muhimman abubuwan da suka sanya a gaba a manufofin harkokin wajen kasar Iran.
Kanaani ya bayyana nahiyar a matsayin matattarar sahihan mutane masu ‘yanci da gwagwarmaya.
A ranar Asabar din da ta gabata kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani ya bayyana cewa, mayar da hankali wajen mu’amala da nahiyar Afirca a matsayin daya daga cikin muhimman manufofin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A kwanakin baya ministan harkokin wajen Iran Hussein Amir Abdollahian ya ziyarci Bamako babban birnin kasar Mali, kuma takwaransa na Mali Abdullah Diop ya tarbe shi, a wani rangadin da ya kai kasashen Afirca da ya hada da kasar ta Mali, Tanzania da Zanzibar.
READ MORE : Ministan Tsaron Taliban; Amurka na kai wa Afghanistan hari daga sararin samaniyar Pakistan.
Bayan haka, Kanaani ya jaddada cewa, “Afirca yanki ne mai matukar muhimmanci a gare mu, kuma fadada alaka da ita na daga cikin abubuwan da Tehran ta sa gaba.
READ MORE : An tsawatar da shugaban Mossad kan kalaman da ya yi game da Iran.