Iran; Hukumar IAEA Taki Bayyana Hadin Kan Da Iran Ta Bata A Rahotonta Na Baya-Bayan Nan.
Jakadan Iran a MDD ya bayyana cewa rahoton hukumar IAEA mai sanya ido a kan harkokin nukliya ta MDD na baya-bayan nan ya nuna bangare ne kawai na yawan tataccen yuranium wanda kasar Iran take samarwa, amma yak i ya bayyana irin hadin kan da Iran ta bawa hukumar a bangaren wasu ayyukanta ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammad Reza Ghaebi yana fadar haka a jiya Litinin bayan da hukumar ta IAEA ta gabatar da sabon rahotonta dangane da shirin nukliyar kasar Iran. Reza Ghaebi ra hoton ya nuna cewa Iran ta ninka har sau 18 yawan tattaccen yuranium wanda yarjejeniyar JCPOA ta amince mata da tace wato kilogram 300 kacal.
Rafael Grossi, daraktan hukumar ta IAEA a rahoton ya bayyana cewa Iran ta ci gaba da tace makamashin yuranium wanda ya wuce kasha 3.67 kamar yadda aka amince mata a yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2015.
Y ace rahoton Grossi dai-dai ne da wanda wakilin tarayyar turai ya gabatar kafin zagaye na uku na tattaunawan dangane da shirin nukliyar kasar ta Iran. Bai ambaci dukkan hadin kan da Iran ta bayar na ganin wasu bangarori na shirin nukliyar kasar ba.
Daga karshe jakadan ya bayyana cewa babu adalci a cikin rahoton ha babban sakataren na hukumar IAEA.