Iran; Girgizan Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 4.4 Ta Aukawa Yankin Qasre-Shirin.
Cibiyar auna girgizan kasa ta kasar Iran da ke jami’an Tehran ta bada sanarwan cewa girgizan kasa mai karfin ma’aunin Richter 4.4 ta aukawa yankin Qasre–Shirin a lardin Kermanshah a safiyar yau Lahadi har sau biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa girgizan kasar ta auku ne da misalign karfe 10:22 na safe, kuma a kan longitude 45.62 da kuma latitude 34.65.
READ MORE : Texas – Shugaba Joe Biden zai Ziyarci Makarantar Robb Dake Uvalde.
Zurfin girgizan kasar ya kai kilomita 10 karkashin kasa, har ya zuwa lokacin bada wannan labarin babu wani bayani dangane da asarorin da aka yi na rayuka ko dukiyoyi.
READ MORE : Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Christian Marc Kabore.
READ MORE : Bachelet – Musulmai A Yankin Xinjiang Na Rayuwa Daban Da Ta Mutane.
READ MORE : Jamhuriyar Afirka Tsakiya – ‘Yan Majalisa Sun Soke Hukuncin Kisa.