Iran; Dole Ne Amurka Ta Ba Da Tabbaci Daga Majalisa Kan Yarjejeniyar Nukiliya.
Mafi yawan ‘yan majalisar dokokin Iran sun ce domin samun nasara ga sabuwar yarjejeniya kan farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015, dole ne gwamnatin Amurka ta ba da wani kwakkwaran tabbacin kan ba za ta sake ficewa daga wannan yarjejeniya ba.
Wannan ya zo ne a wata sanarwa da wakilai sama da 250 na majalisar dokokin Iran suka sanya wa hannu a jiya Lahadi, wadda ta mayar da hankali kan halin da ake ciki a tattaunawar da ake yi a Vienna babban birnin kasar Ostiriya kan batun farfado da yarjejeniyar, wadda aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA).
‘Yan majalisar sun ce gogewar da aka samu a zagayen da ya gabata a Vienna na nuni da cewa rashin amincewar Amurka da sauran bangarorin da suke tattaunawa kan bayar da lamunin da ya dace, shi ne babban abin day a zama karfen kafa ga ci gaban tattaunawar.
READ MORE : Tunisia ; Zanga zangar Kin Jinin Shugaba Kais Saied, Na Dada Kamari.
Bayanin ya ce, dole ne majalisar dokokin Amurka ta amince a hukumance da yarjejeniyar, kuma ta bayar da tabbaci a kan cewa gwamnatin Amurka ba za ta sake ficewa daga yarjejeniyar ba.