Iran Dole A Cire Mata Dukkan Takunkumi Kafin Cimma Yarjejeniyar Vienna.
Shugaban kasar iran Ibrahim Ra’isi shi ne ya furta hakan a lokacin tattaunawarsa ta wayar tarho da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron , ina ya nuna cewa duk wata yarjejejniyar da za’a cimma a tattaunawar Vienna dole ne a cire dukkan takunkumin da aka kakabawa Iran tare da bada lamuni
A tattaunawar taso ta wayar tarho dukkan shuwagabannin kasashen Biyu sun tattauna kan ci gaban da ake samu a tattaunawar ta Vienna tsakanin iran da kasashen Turai 5, Shugaban na Iran ya fadi cewa tawagar iran a tattaunawar sun sha nanata cewa tana maraba da duk wani yunkuri da zai kare hakkin Alummar iran
Iran ta nuna cewa ba za ta amince da wani abu da ya gaza cire mata dukkan takunkumi ba da kasar Amurka ta kaka ba mata ba , kuma tana bukatar a bata lamunin cewa Amurka ba za ta kara yin watsi da yarjejeniyar ba a nan gaba.
Ko a ranar Alhamis da ta gabata ma jagoran juyin musulunci na iran imam Khamna’I ya fadi cewa makiya suna son kange iraniya daga hakkinsu na mallakar makamashin nukiliya don Ayykan zaman lafiya, kana ya nanata cewa iran ba ta nufin mallakar makamin nukiliya kwata –kwata