Iran; Dakarun Kare Juyin Musulunci Sun Gargadi Isra’ila Kan Sake Wasu Kura-Kurai Dangane Da Tsaron Kasar.
Manjo Janar Husain Salami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gargadi HKI da kakkausar murya, dangane da sake keta hurumin tsaro na JMI.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Salami yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatara jana’izar da aka yiwa wasu sojojin kasar a ranar Laraba.
Salami ya kara da cewa, idan HKI ta sake wannan kuskuren ta kuwa zata fuskanta maida martani da makamai masu linzami na dakarunsa.
READ MORE : MDD; Kwamitin Tsaro Ya Ki Amincewa Da Shawarar Rasha Ta Tsagaita Bude Wuta A Ukrain.
Kafin haka dai a farkon wannan watan ne jiragen yakin HKI suka kai farmaki kan sojojin kasar a sansaninsu dake kasar Syriya inda sojoji mbiyu suka yi shahada.
Bayan wasu kwanaki dakarun suka maida marta da makamai masu linzami har 12 kan cibiyar leken asiri na HKI dake birnin Arbil na yankin kurdawan kasar Iraki da makamai masu linzami masu karfin gaske wadanda suka wargaza cibiyar.