Iran; Dakarun IRGC Sun Kame Wani jirgin Ruwa Da Ke Fasa-Kwaurin Danyen Mai A Cikin Tekun Fasha.
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun sha alwashin cewa tekun Fasha ba zai taba zama mafaka ga masu fasa-kwauri ba.
Bayanin ya ce rundunar ta ce ta kama wani jirgin ruwa na kasashen waje a yankin arewacin hanyar ruwa yana safarar danyen man fetur da ya kai lita 200,000 a karo na uku a cikin wannan watan.
Shugaban sashen hulda da jama’a na shiyya ta biyu na sojojin ruwa na IRGC Kanar Gholam Hossein Hosseini, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Fars a jiya Lahadi cewa, an kama ma’aikatan jirgin 8 da aka kai su birnin Bushehr da ke tashar jiragen ruwa na kudancin Iran, inda za a mika shi ga hukumomin shari’a don gudanar da cikakken bincike.
Jami’in na IRGC ya lura cewa yaki da safarar man fetur shi ne babban abu mafi muhimmanci ga rundunar sojojin ruwa ta IRGC bisa la’akari da cewa hakan zai tallafawa kasar da ma sauran kasashen yankin wajen magance matsaloli irin wadanann da suke fuskanta.
Hosseini ya jaddada cewa gabar Tekun Fasha da ruwan da ke kewaye da ita “ba za su taba zama wuri mai aminci ga masu cin riba ta hanyar fasa-kwauri ba.”