Iran Da Venezuela Sun Jaddada Wajabcin Kara Karfafa Kawance Da Alakoki A Tsakaninsu.
Shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya bayyana cewa, kara habaka alaka tsakanin Iran da Venezuela da kuma ci gaba da yin tsayin daka wajen kare hakkokinsu, shi ne babban makaminsu da zai kai su ga samun babbar nasara.
A cikin sakon da ya aike wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro a jiya Talata, Raeisi ya ce yana da tabbaci kan cewa za a samu nasara ta hanyar fadada huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaba da yin tsayin daka da suke yi wajen fuskantar bukatun wuce gona da iri na ‘yan mulkin mallaka.
Wannan na zuwa ne a cikin sakon taya murna ga shugaban kasar Venezuela da al’ummar kasar dangane da zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar, da Ibrahim Ra’isi ya aike, inda kuma ya cewa, salon da Venezuela take tafiya a kansa na zama kasa mai cikakken ‘yancin siyasa, yana nuni ne da kokarin da Simon Bolivar, gwarzon kwatar ‘yancin kai na kasashen kudancin Amurka ya yi a karni na 19, kuma a halin yanzu Venezuela babban misali ce a kan sadaukarwarsa, da kuma kin mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin mallaka.
Raeisi ya ce “Wannan rana mai cike da tarihi wata alama ce ta kokarin da kasashe masu neman ‘yanci ke yi na kawar da mulkin mallakar kasashe masu girman kai na duniya.”
Shugaban na Iran ya bayyana fatan cewa Tehran da Caracas za su kara inganta dangantakar abokantaka da dabaru da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya.
A ziyarar da shugaban kasar Venezuela da ya kai a kasar ta Iran a watan da ya gabata, Tehran da Caracas sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta shekaru 20 da nufin karfafa hadin gwiwa a bangarori daban-daban, musamman a fannin kimiyya, fasaha, aikin gona, man fetur da iskar gas, sinadarai na man fetur, yawon bude ido da kuma al’adu.