Iran Da Turkmenistan Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyi Don Bunkasa Hulda A Tsakaninsu.
Gwamnatin kasar Iran da kuma Turkmenistan sun rattaba hannu kan yarjiniyoyi don bunaka hulda tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, shugaban kasar Iran Syyid Ibrahim Ra’isi da kuma tokwaransa na kasar Turkmenistan Serdar Berdimuhamedow ne suka sanya ido a lokacinda jami’an gwamnatin kasashen biyu suke rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a safiyar yau Laraba.
Kafin haka dai shugaban Ra’isi ya yiwa tokwaransa, wanda ya isa nan Tehran a jiya Talata, na kasar Turkmenistan tarba ta musamman, kafin sanya hannu kan yarjeniyoyin.
READ MORE : Tel Aviv ta isa Riyadh don tunkarar Iran.
Shugaban kasar Turkmenistan dai ya fara ziyarar kwnaki biyu a nan Tehran tun jiya Talata, kuma ana saran banda sanya hannu da aka yi a safiyar yau Asabar kan yarjeniyoyi, kasashen zasu bukaci kara fadada dangantaka da ke tsakanin klasashen biyu ta bangarorin kasuwanci sifili yawon shakatawa da kuma noma.
READ MORE : Sudan – Mutane Sama Da 100 Sun Mutu Sakamakon Rikicin Kabilanci.
READ MORE : Iran Ta Kare Matakin Da Ta Dauka A Kan Kudirin Hukumar IAEA.
READ MORE : Kwalara Ta Kashe Sama Da Mutane 150 A Kamaru – MDD.