Iran Da Rasha Sun Kudiri Aniyar Yin Watsi Da Dalar Amurka A Cikin Harkokinsu Na Cinikayya.
A yayin ganawarsa da shugaban kasar Rasha Valadimir Putin a yammacin jiya, jagoran juyin juya halon muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran da Rasha za su yi watsi da dalar Amurka a cikin harkokin kasuwanci da nikayya da suka hada kasashen biyu.
Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, jagoran juyin juya halon muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya sheda wa shugaba Putin cewa, yin aiki kafada da kafada tsakanin Iran da Rasha a dukkanin bangarori na babban tasiri wajen dakushe babakeren kasashe da ke bautar da duniya ta hanyar siyasa da tattalin arziki.
Haka nan kuma jagora ya bayyana abin da ke faruwa a Ukraine a matsayin wani abu da kasashen NATO suka haddasa, sakamakon yadda suke hankoron haifar da fitunu a yankin, da kuma tsokanar kasar Rasha.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya jaddada matsayin kasarsa na karfafa kwawancenta da kasar Iran, domin samun daidaito a cikin siyasar yankin da ma duniya, kamar yadda kuma ya bayyan acewa babakeren kasashen yammaci a kan duniya ya kawo karshe.